Daga Ibrahim Sani Gama
Wasu mabiya Shi’a a jihar kano sun roki gwamnati da jami’an tsaro a jihar kano da su Basu kariya don su gudanar da harkokin addininsu kamar yadda dokar kasa ta baiwa kowanne dan Nigeria.
Kadaura24 ta rawaito Sulaiman Gambo shi ne ya bayyana hakan lokacin taron manema labarai da suka gudanar a nan Kano a ranar Asabar.
Sulaiman Gambo yace a jiya juma’a wasu batagari sun je Inda suka gudanar da karatuttukansu da addu’o’i suka bankawa makarantar wuta ba tare da sun bar ko tsinke ba a cikin makarantar.
” Wasu da muke Zargin tunzura su akai sun zo sun gone mana kayiyaki Masu tarin yawa, wadanda suka hadar da janareto da litattafai da sauran kayan koyo da koyarwa da ma Sauran kayan amfani na yau da kullum suka Tara su wuri guda suka sa taya sannan suka gone su kurmu”. Gambo
Yace lamarin dai ya faru ne a wata makarantarsu dake unguwar Dorayi babba, Inda ya ce Wannan ba shi ne karon farko ba da aka yi musu irin wannan mummunan aikin wanda yace ba addinin musulunci ne ya koyar da su ba .
Kishi: Wata Mata ta Kashe Tsohon Mijinta a Jihar Kebbi
“Akwai wasu limaman masallatan juma’a da muke Zargin sune suka tunzura wadanda suka yi mana waccan ta’adi wanda yasa mukai asarar kimanin Naira Miliyan 3 da wani Abu” inji Sulaiman Gambo
Rundunar Sojin Nigeria ta Kori Sojojin da ake Zargi da Kisan Wani Malami a Yobe
Yace daman a bayan sun kai Kara wajen jami’an tsaro har ma tsohon kwamishinan yan sanda wanda ya ajiye aiki ya bada umarni ga DPO na Chaji ofis din Yan sanda na Dorayi babban da ya gudanar da bincike kan abubuwan da ake yi mana.
” Mu fa bama son tashin hankali saboda mu Musulmi Kuma musulunci ya hana tashin hankali, Amma ana so a hana mu damar da kundin tsarin mulkin kasar nan ya bamu na kowa yayi addinin da yake so cikin yan me yasa mu za’a rika yi mana haka?”.
Sulaiman Gambo ya suna kira da duk Masu fada a ji a yankin unguwar Dorayi babban da sauran masu ruwa da tsari da dauki matakan hana afkuwar hakan a nan gaba domin yin hakan shi ne zai tabbatar da dorewar Zaman lafiyan da ake da shi a jihar kano.