Daga Maryam Adamu Mustapha
Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya musanta labarin cewa a anar Litinin dinnan zai fice daga jamiíyyar NNPP zuwa PDP kamar yadda wasu ke ta yadawa a kafafen sada zumunta.
Sanata Shekarau ya bayyana haka ne yayin taron da ya gudanar da yan kwamitinsa na shura na kananan Hukumomin 44 a Kano a ranar Litinin.
“Har yanzu ina nan a NNPP, amma yadda ake ci gaba da samun rashin adalci da kuma rashin cika alkawarin da aka kulla da alamu nan gaba kadan zan bayyana matsaya ta karshe kan batun zama ko kuma ficewa daga NNPP” inji Shekarau
Malam Ibrahim shekarau ya kuma ce ko shakka babu jami’iyyu daban-daban sunyi zawarcinsa, domin ya yi musu takarar mataimakin dan takarar shugaban kasa, amma bai aminta da tayin da akai ma sa ba.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da suyi hakurin kammala jiran rahotan karshe na shugabancin kwamitin shura, wanda dama sune ke nuna inda alkibilarsa a siyasance ke kasan cewa.
“Muna bin koyar addinin musulunci da yace duk abun da mutum zai yi yayi addu’a sannan ya shawarci makusantansa, sannan sai ya barwa Allah zabi akan, Kuma duk abub da Allah ya zama masa sai ya karba yayi godiya”. Inji Shekarau
Rundunar yan sanda ta turo sabon Kwamishinan yan sanda jihar kano
Sanatan Kano ta tsakiya Malam ibrahim Shekarau ya ce sai da aka yi masa tayin dala miliyan ɗaya ($1,000,000), kan ya koma wata jam’iyya amma bai karɓa ba, shekarau na wannan furuci ne a wajen taron majalisar shura da aka gudanar a litinin ɗin nan, biyo bayan rikicin cikin gida da jam’iyyar NNPP take fama dashi.
Tunda fari dai jaridar dailyNigeria ta rawaito cewa Sanata Shekaran na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP zuww PDP biyo bayan zargin hana ƴan fadar mundubawa takara a matakai daban daban, zargin da Jagoran Jam’iyyar ta NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya musanta, a cewar sa ɓangaren Malam Ibrahim Shekarau sun shiga jam’iyyar NNPP ne lokacin da an riga an gama fitar da ƴan takarkaru, saidai Kwankwason yace an yiwa tsagin na shekarau alkawarin mukamai idan an kafa gwamnati a matakin jiha.
Majalisar dokokin Kano ta amince da sabbin kwamishinonin da Ganduje zai naɗa
Toh sai dai kalaman na Sanata kwankwaso bai yiwa tsagin na Malam Ibrahim shekarau daɗi ba, wanda hakan ta sanya kwamitin shura na gidan sanata Shekarau fara tattaunawa dan nemowa kansu mafita.
A yayin taron da yayi da magoya baya litinin ɗin nan, Shekarau ya ce ceto al’ummar Kano daga halin da suke ciki ne ya sanya su shiga jami’iyyar NNPP ba bukatar kai ba, domin idan dan biyan bukatar kai ne anyi masa tayin dala Miliyan ɗaya amma bai karba.
Toh sai dai a taron, Sanata Shekarau bai bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ta NNPP ba, amma dai ya tabbatar da cewa nan gaba kaɗan zai bayyana matsayar sa.