Daga Rukayya Abdullahi Maida
Majalisar ta Shura ta gidan Siyasa Malam Ibrahim Shekarau, ta gindaya sharuddan sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Sharuɗɗan sun kasance wani ɓangare na rahoton Shura da za a gabatar wa Malam Shekarau a yau Asabar .
Jaridar DAILY NIGERIAN ta bayyana shirin Malam Shekarau na ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP duk da samun tikitin takarar sanata da yayi
Lokacin da Malam Shekarau ya bayyana batun tattaunawar da yake yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, da kuma tayin da aka yi masa a gaban yan kwamitin Shura, rahotannin sun bayyana cewa sai da majalisar ta dare gida biyu.
![](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2022/08/FB_IMG_1661018964453-300x225.jpg)
Yayin da wasu suka bayyana ra’ayinsu na sauya sheka zuwa PDP, wasu kuma sun goyi bayan matakin na Malam Shekarau saboda “NNPP ta kasa baiwa mutanen Mallam gurbin takara a jam’iyyar.
Ganduje zai nada matashi mai shekaru 33 kwamishina a kano, waye shi ?
Wata majiya mai tushe da ta so a sakaya sunanta ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa a wani bangare na tayin da aka yi na neman Malam Shekarau, Atiku Abubakar ya yi alkawarin nada shi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya ko kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Majiyar ta kara da cewa Malam Shekarau ne zai jagoranci yakin neman zaben jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma, tare da bayar da umarnin kai wa shugabannin addini da na gargajiya goyon baya.
“Ka san Mallam yana da kyakyawar alaka tsakaninsa malaman addini da sarakunan gargajiya a Arewa, idan Mallam ya jagoranci yakin neman zabensa a Arewa Atiku zai samu saukin samun goyon baya Malamai da sarakuna,” inji majiyar.
A makon da ya gabata ne aka kafa wani kwamiti mai mambobi 21 don yin nazari kan wannan shawara tare da bayar da rahoto kan ci gaban da aka samu.
Sai dai wani babban na hannun daman Malam Shekarau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar cewa ba Sanatan ne ya zo da bukatar sauya sheka ba, manyan Arewa ne.
A cewar majiyar, batutuwa biyu – matsin lamba daga manyan Arewa da abokansa – ya sanya Malam Shekarau ya koma PDP.
“Mallam ya damu musamman saboda gunaguni cikin gida game da yadda yake son kansa ba tare da nemawa mutanensa mukamai. Yayin da Malam yake kokarin shawo kan rikicin cikin gida, sai dattawan Arewa suka fara kiransa da ya zo ya hada kai da Atiku,” inji majiyar.
Mai magana da yawun Malam Shekarau, Sule Ya’u Sule, wanda tun da farko ya shaida wa manema labarai cewa za a yanke shawara a cikin makon nan, ba a samu damar jin ta bakinsa ba dai har yanzu.