2023: Takarar Sha’aban Sharada nake goyon baya a ADP Kuma zan bashi gudunmawa har ya ci zabe – Rarara

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Shahararren mawakin Siyasar nan Alhaji Dauda Kahutu Rarara yace ya dauki Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin Dan takarar sa na gwamna a  zaben shekara ta 2023 .

 

Kadaura24 ta rawaito Rarara yace yana da dalilai Masu yawa da suka sa zai goyi bayan takarar gwamnan kano ta Sha’aban Ibrahim Sharada.

 

Dauda Kahutu Rarara ya bayyana hakan ne yayin Wani taro da Sha’aban Sharada ya shirya a Kano .

Ganduje zai nada matashi mai shekaru 33 kwamishina a kano, waye shi ?

” A cikin dalilai na ko da daya na dauka ya isheni hujjar goyon bayan takarar Sha’aban Sharada, Amma yanzu lokaci bai yi ba da zan bayyana ba, nan gaba kadan zan fada kowa ya ki”. Inji Rarara

“Ina Wannan tafi Kuma da ni za’a yi ta har lokacin da Zamu je a rantsar da Sha’aban, zan Kuma bada gudanarwar wakoki kamar su “Malam Sha’aban” da Kuma Dan Karamin sauro”. Inji Rarara

 

Shura ta baiwa Shekarau sharudda 5 na sauya sheka zuwa PDP

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Sha’aban Sharada ya fice daga jam’iyyar APC Inda ya koma jam’iyyar ADP Kuma har ya sami takarar gwamnan Kano a jam’iyyar.

 

Abun mamakin dai shi ne yadda Rarara ya yi Shura wajen yiwa jam’iyyar APC wakoki da Kuma goyon bayan takarar Bola Tinubu a matsayin dan takararsa na shugaban kasa wanda kuma dan jam’iyyar APC ne, kwatsam sai ga shi ya bayyana goyon bayan takarar sa a jam’iyyar ADP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...