Daga Yakubu Abdullah
Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje zai nada kwamishinan zai Fi kowanne kwamishina karancin Shekaru a kasar nan a kokarin sa na ganin ya baiwa matasa dama a cikin gwamnatin sa.
Dr. Yusuf Jibril JY na daga cikin sabbin kwamishinonin da Gwamna Ganduje ya aikowa Majalisar dokokin jihar kano sunansu domin tantancesu don ya nada su a matsayin kwamishinoni.
idan za’a iya tunawa kungiyoyin matasa daban-daban na cikin gida dana waje a kowanne lokaci sukan yi kiraye-kiraye ga shugabannin a matakai daban-daban don su rika sanya matasa cikin kunshi gwamnatinsu, musamman manyan mukai Kamar mukamin kwamishina da dai sauransu.
Za’ai kwana uku ana ruwan sama a wasu jihohin Nigeria – Hukumar kula da yanayi
A wannan karon gwamna Ganduje ya tasamma cika wancan buri ba matasa ta hanyar dauko Matashin wanda bai wuce shekaru 33 ba a duniya Inda zai nada shi mukamin kwamishina bisa la’akari da wasu managartan halaye da kwarewar Dr. Yusuf Jibril a harkokin kasuwancin da Kuma zamantakewar rayuwa.
waye Dr. Yusuf Jibril JY
Dr. Yusuf Jibril dan asalin garin rurum ne a karamar hukumar Rano ne ta jihar kano, ya yi karatun firamare sakandire har ya kai digirin digirgir, Kuma Kwararren lititane Kuma Mai harkar sufurin dakon Mai ta karkashin kamfaninsa mai suna JY Global services .
bayan ga kasancewarsa Dr. Yusuf Jibril hamshakin Mai harkar sufurin dakon Mai ne a kasar nan da yake da ma’aikata Masu tarin yawa a karkashin sa, ya kasance Dan siyasa mai kishin ganin al’ummarsa sun samu kyakyawar rayuwa ta hanyar sama matasa aiyukan yi da burin ganin sun sami ababen more rayuwa a yankinsu.
Ban taba da na sanin ajiye mukamin kwamishinan a gwamnatin Ganduje ba – Shehu NaAllah
Idan Allah ya tabbatar da Dr. Yusuf Jibril a matsayin kwamishina za’a iya cewa tarihi ya sake maimaituwa a jihar kano, idan za’a iya tunawa lokacin da Audu Bako yana gwamnan Kano, ya dauko Alhaji Aminu Alhassan Dantata a shekarar 1968, lokacin yana da karancin shekaru Kuma gashi attajiri ya bashi mukamin kwamishinan kasuwan, wanda hakan yasa aka samu gagarumar nasara a bangaren kasuwanci a jihar kano.
Babu shakka tarihi ba zai manta da irin gudunmawar da Alhaji Aminu Dantatyya bayarba wajen cigaban kasuwanci da jihar kano, Kuma hakan ta faru ne saboda gogewa da iya mu’amala da Kuma Rashin kishirwar samun abun duniya da Alhaji Aminu Dantata yake da su.
Haka al’umma suke sa ran za’a sami cigaba mai tarin yawa idan aka baiwa Dr. Yusuf Jibril mukamin kwamishinan saboda matashi ne kuma attajiri Kuma gogaggen dan kasuwa kum Kwararren likita, don haka idan ya zama kwamishinan kowacce ma’aikata akwai kyakyawan yakin zai bada gudunmawa don cigaban jihar kano.
kan batun hidimtawa al’umma Dr. Yusuf Jibril yakan bar duk wasu aiyukansa aje asibitoci yankin domin duba marasa Lafiya kyauta ba tare da ya karbi ko sisin kobo ba, attajiri ne da yake amfani da dukiyar da Allah ya bashi wajen hidimtawa al’umma.
A Siyasance Dr. Yusuf Jibril ana ganin zai taka muhimmiyar rawa wajen cin nasarar jam’iyyar APC musamman a yankin Rano Kibiya da Bunkure saboda Dan Siyasa ne da yake taimakawa al’umma ba tare da la’akari da jam’iyyar ba.
Kuma zai cike gibin da jam’iyyar APC ta samu a yankin saboda kwarewarsa da kuma kyakyawar mu’amalarsa da al’umma da ma farin jinin da yake da shi a wurin al’ummar yankin Rano Kibiya da Bunkure.
Ya zama wajibi a yabawa gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje saboda hangen nesan da ya yi wajen zabo wannan bawan Allah Dr. Yusuf Jibril JY , wanda aka hakikance zai bada gudunmawa wajen cigaban yankin Rano Kibiya da Bunkure da ma jihar kano baki daya.