Ban taba da na sanin ajiye mukamin kwamishinan a gwamnatin Ganduje ba – Shehu NaAllah

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

tsohon kwamishinan kudi na gwamnati jihar kano Hon. Shehu Na’Allah kura yace bai taba da na sanin ajiye mukamin sa na kwamishinan kudi a gwamnatin Ganduje ba, saboda ya aminta da cewa yayi abun da ya dace

 

“Na ajiye mukamin ne Saboda Mai gidana wanda nake yiwa biyayya a Siyasa ya fita daga jam’iyyar, ni kuma naga bai dace ya bar wajen ba ni in cigaba da zama a wajen ba, don haka bana dana Sani don nayi abun da ya dace a sanda ya dace”. Inji Shehu Na’Allah kura

 

Kadaura24 ta rawaito Shehu Na’Allah kura ya bayyana hakan ne a wata tattauanawa da akai da shi a wani shirin Siyasa Mai suna Siyasar Kano sai kano wanda ake gabatarwa a gidan Radio tarayya Pyramid FM dake Kano.

 

Za mu ci zaɓe a 2023 duk da matsalolin tsaro a Nijeriya — Abdullahi Adamu

tsohon kwamishinan wanda tsohon Shugaban karamar hukumar kura ne ya ce a Siyasa bashi da jagoran da ya Fi Malam Ibrahim Shekarau Kuma shi yake yiwa biyayya a kowanne irin al’amari na Siyasa a Kano.

 

Nasiru Ali Ahmad zai gyara makarantar Govt. Tech. College Kano don samawa matasa aiyukan yi

“Nabi Shekarau ne a dai-dai lokacin da yake yake tsananin bukatar masoyansa su bishi na Kuma bishi jiya yau ma shi zan bi gobe da jibi ma dole shi zan bi, saboda ya kaunaceni Kuma Nima bani da abun da zan yi masa sai in kaunace shi in Kuma yi masa biyayya a dukkan umarnin sa”. inji Kura

 

Shehu Na’Allah ya bada tabbacin zai bi Shekarau duk jam’iyyar da ya koma, sai dai yace bai kamata mutane su rika kokarin shiga tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kwankwaso ba, saboda su kadai suka San abubuwan da suke tattunawa idan sun shiga daki sun kulle.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...