Tashar tsandauri ta Dala: Gwamnatin Kano ta bada gudumawar naira biliyan 2 don kammala aikin – Gawuna

Date:

Daga Siyasa Ibrahim

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta bayar da gudunmowar kimanin naira biliyan biyu da miliyan biyar domin gina tituna, katanga, samar da wutar lantarki da sauran ababen more rayuwa a aikin tashar tsandauri ta Dala domin ganin an kammala shi cikin akan lokaci.

 

Mukaddashin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin da ministan sufuri Alh.Mu’azu Jaji Sambo ya kai ziyarar gani da ido tashar ta Dala Inland Dry Port da ke Zawaciki a karamar hukumar Kumbotso.

 

Ya ce gwamnatin jihar kano ta tabbatar da cewa aikin ya tabbata ta hanyar samar da kyakyawan yanayi, domin hakan zai haifar da ci gaban tattalin arziki ba kawai ga Kano da jihohin da ke makwabtaka da ita ba, har ma da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi.

 

Talla
Talla

Gawuna ya kara da cewa Kano ita ce cibiyar kasuwanci da zuba jari a Arewacin Najeriya kuma ita ce mafi girman tattalin arzikin cikin jihohin da basu da mai da iskar gas, da take juya kusan dalar Amurka biliyan goma sha biyu wanda hakan ya sa za a iya janyo hankalin masu zuba jari.

A Sanarwar da babban Sakataren yada labaran mukaddashin gwamnan Hassan Musa Fagge ya aikowa kadaura24,yace Gawuna yace ana yin hakan nufin amfani da albarkatun jihar don inganta rayuwar al’umma, Ya kara da cewa hakan ya zama dole idan aka yi la’akari da yadda kudaden shigar danyen mai da kasar da ake dogaro da su su ragu matuka.

An kaddamar da tashar tsandaurin ne ta Dala Inland don yin aiki a matsayin mai hanyar ba da gudummawa don inganta harkokin kasuwancin cikin gida da na waje da kuma farfado da fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen waje don inganta da tattalin arzikin jihar kano dana kasa baki daya.”

 

Talla
Talla

A nasa jawabin Ministan Sufuri, Engr.Jaji Sambo yace samar da tashar tsandaurin a Kano yayi matukar dacewa kasancewar Kano cibiyar kasuwanci da take da Kamfanin masaku da masana’antu daban-daban, wadanda idan aka fara aiki da tashar tsandaurin Zata taimakawa dukkanin al’ummar Kasar nan baki daya .

A cewarsa an samar da tashar ne a shirin gwamnatin tarayya na sake fasalin tashoshin jiragen ruwa da aka tsara domin rage cunkoso tashoshin jiragen ruwa tare da daukar ayyukan sufuri da jiragen ruwa kusa da masu shigo da kaya da masu fitar da kaya a yankin, duk da haka tashar ta Dala ta yi shekaru da yawa ana yinta Amma yanzu ta tabbata.

Sai dai ya yabawa gwamnatin tarayya da gwamnan jihar Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen ganin aikin ya tabbata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...