2023: Tafiyar Atiku ta kowa ce, ku haɗa kai don mu sami nasara – MaiKano Chiromawa ya fadawa kungiyoyin PDP

Date:

Daga Safiyanu Dantala jobawa

 

An bukaci magoya bayan jam’iyar PDP a duk inda suke, da su hada kansu don cimma nasarar zabe mai zuwa na 2023 a kasar nan.

Mataimakin coordinator na neman zaben Atiku Abubakar Turakin Adamawa, Hon Abdullahi Maikano Chiromawa (Jarman-Garun malam) shi ne ya bukaci hakan, a lokacin da yake cigaba da ganawa da ‘ya’yan jam’yar PDP na jihar kano.

Talla
Talla

 

Ya ce duk wata nasara ba ta samuwa sai ana da da kyakkyawan hadin kai da amana a tsakanin magoya baya.

 

A Wannan karo MaiKano Chiromawa ya  ya gana ne da ‘ya’yan kungiyar People’s Democratic Party National Youth Agenda PDP-NYA reshen jihar Kano tare da shugaban ATIKU/OKOWA UNIFIER PROJECTS Najib Nasir a ofishin tafiyar ATIKU/OKOWA 2023 dake Gyadi-Gyadi lan titin Zaria,Kano.

Kungiyar Kanam Media Hub ta horas da mata yan jaridu dabarun aiki a Kano

 

A karshe ya yi wa kungiyoyin tafiyar da alkawarin basu gudunmawarsa don cigabansu da al’ummar kasa baki daya matukar Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya lashe zaben shekara ta 2023 me zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...