Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban karamar hukumar Kwumbotso Hon Hassan Garban Kauye ya yabawa gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa jajircewarsa wajen ganin ya samar da ingantaccen Ilimi ga al’ummar jihar nan.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana haka ne a jiya litinin a yayin ziyarar bazata da ya kai wurin da ake gudanar da aikin tantance wadanda zasu ci gajiyar tallafin karatu na gwamnatin jiha da aka gudanar a harabar Sakatariyar Karamar Hukumar.

Ya kuma yabawa kokarin kwamitin karkashin jagorancin sakataren karamar hukumar Yahaya Bala Chalawa bisa jajircewar da suka yi wajen gudanar da aikin, inda ya bukace su da su tabbatar da bin duk ka’idojin da aka tanadar wa daliban da suka cancanta.
Rayuwa ta tana cikin Hadari -Hadiza Gabon
A Sanarwar da Mai taimakawa Shugaba karamar hukumar kan harkokin kafafen yada labarai Shazali Saleh farawa ya aikowa kadaura24 yace, Shugaban ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar Makarantar Sakandare ta jiha da su yi amfani da alawus din ta hanyar da ta dace.