A zagayen da mukai na fahimci matsalolin kano kuma zan magance su idan na zama Gwamna – Salihu Tanko Yakasai

Date:

Daga Shehu Sulaiman Sharfadi

 

Dan takarar Gwamna a jamiyyar PRP Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya jaddada aniyarsa ta cigaba da kai ziyara kananan hukumomin jihar nan don sanin halin da yankunan suke domin ya san ta yadda zai tunkari matsalolin idan ya zama gwamna.

 

Yakasai ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin Kadaura24 a nan kano.

 

Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa sun zagaya kananan hukumomin jihar nan don ganewa idonsu halin da al’ummar wadannan yankunan ke ciki, wanda da zarar Allah ya basu nasara babban zaben shekara ta 2023 zasu yi iyaka bakin kokarinsu wajen magance matsalolin dake addabar yankunan .

Talla

 

Ya kuma bayyana cewar wannan ziyara ta kunshi sada zumunci da neman tubarrakin manyan kowacce Karamar hukuma kamar malamai da hakimai da dagatai da masu unguwanni.

Da dumi-dumi: Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi sun yi kicibis a Abuja

yace sun kuma ziyararci da dama daga tsofaffin jagororin jamiyyar tun lokacin da take NEPU.

 

Ya kuma bayyana cewar nan bada jimawa jam’iyyar zata kai ziyara mazabu dari hudu da tamanin da hudu don duba halin da ya’yan jam’iyyar da al’ummar yankin su ke ciki.

Rundunar yan sanda ta haramtawa Yan fim amfani da kakinsu a fina-fina

Dan takarar Gwamnan ya kuma baiwa magoya bayansu dama sauran al’ummar jihar nan tabbacin idan P R P ta kafa gwamnati zasu sauko kasa don tafiya da kowa ta hanyar sauraron matsalolin al’umma tare da ganin ta tabbata magance musu shi.

 

Daganan sai yayi kira ga yan takarkarinsu da su cigaba da bashi hadin kai da goyon baya dari bisa dari, wajen ganin an cimma nasarar da ake da bukata, inda yace shi kansa zai iya tafiyar da al’amuran jamiyyar ba ba tare da goyon bayan su ba.

 

Daga karshe Sai ya bayyana farin cikinsa tare da taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar sabuwar shekarar musulunci, inda yayi fatan Allah ya zabawa kasar nan Shugabanni nagari da kuma samun zaman Lafiya mai dorewa a fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...