Daga Abubakar Sadeeq
A karon farko, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi gaba-da-gaba da Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II tun bayan da Gandujen ya sauke basaraken daga kujerar Sarkin Kano.
Daily Trust ta ce mutanen biyu sun hadu ne a tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe a Abuja a Litinin din nan.

Sai dai jaridar ba ta bayyana ko mutanen biyu sun yi musabaha kamar yadda aka saba kafin 2020, Amma hotunan da suke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yarda Gwamnan suke musabaha da Sarkin Sanusin .