Jami’an tsaro sun kama mutane hudu da ake zargin sun taimaka wajen kai hari gidan yarin Kuje

Date:

Auwal Alhassan Kademi

 

Jami’an tsaron Najeriya sun cafke wasu mutane hudu da ake zargin na kwarmata bayanan sirri ga ‘yan bindiga a babban birnin ƙasar, Abuja.

 

Jaridar PRNigeria ta rawaito wata majiya mai karfi ta hukumar leken asiri ta kasa da ke tabbatar da kamen.

 

Jaridar ta ce an cafke mutanen tare da wasu na’urori da makamai da tsoffin wayoyin hannu da basa amfani da intanet.

Talla

Majiyar da ke cikin ayarin mutanen da suka yi kamen na cewa, ana ci gaba da bincike cikin sirri domin gano shugabanninsu da masu daukar nauyinsu.

 

Waɗannan mahara ake kuma zargi da kai hari a wasu sassan yankunan Abuja, a cewar majiyar.

Asibitin MGK Healthcare ya yi wa sama da mutune 130 Gwajin Cutar hanta kyauta a kano

 

Yanzu haka ana tsare da mutanen da aka cafke da tuhumarsu domin amsa tambayoyi.

 

Jaridar ta kuma rawaito cewa hukumar tsaro ta Najeriya na tattara bayanan sirri domin gano masu hannu a matsalolin tsaro da hare-haren da ake kitsawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...