Daga Abdulhamid Isa D/zungura
27 Yuli, 2022
Shaharran mawakinnan Hausar nan Aminudden ladan Abubakar wanda ake yiwa lakabi da Alan waka, yace ya dauki kimanin shekaru 7 yana rubuta wakar da ya yiwa fiyayyen halitta manzan Allah (S.AW) wadda ya sanyawa suna “Muhammadu miftahul futuhati linzamin rayiwata”.
Alan waka ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da sukai da wakilin Kadaura24 shi a ofishinsa dake zoo road a kano .
Yace ya kwashe wadancan Shekaru ne Yana gudanar da Bincike saboda wakar ta shafi tarihin rayiwar shugaban halitta manzon Allah (S A W) tun daga haihuwa har zuwa wafatinsa.
Wani dan majalisar wakilai ya sha da kyar daga hannu magoya bayan sa a Kano
“Irin wannan babban aiki yana matukar bukatar Bincike na tarihin da kuma irin kalmomin da za’a yi su akan Fiyayyen halitta, don gudun zarmewa”. Inji Alan waka
Hakazalika yace ita waka “Mufitahul futuhati” littafi ne ya mayar da shi waka saboda mutane da dama su amfana kuma babu Shakka mutane sun ji dadin wakar kuma Nima Ina alfahari da ita.
Kassosa ta baiwa dalibai 30 tallafin kayan karatu a makarantu 2 a Kano
Ya ce mafiyawan Wakokinsa yana Yana gina sune da Ilimi kuma yana gudanar da bincike kafin yayi kowacce irin waka, yace domin yin hakan shi yake bashi damar fadin abun da yake dai-dai akan duk wanda zai yiwa waka.
“Ina wakoki sosai na sarakuna na yan siyasa Yan kasuwa da dai sauran su, to duk wanda zan yi waka akan shi nakan nemi tarihin rayuwar sa da irin gwagwarmayar da yayi, don sanar da al’umma sun san cewa mutum baya zama wani sai ya wahalar“.
Alan waka ya bada tabbacin yana bada gudunmawa sosai don ganin kananan mawaka suma sun taso kuma sun yi wakokiisu akan tsarin da ya dace, Inda yace a bayan har makarantar koyar da sha’anin waka yayi Amma ta yanar gizo kafin lamarin ya tsaya.