Auwal Alhassan Kademi
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tarauni, Hafizu Kawu ya tsallake rijiya da baya a wajen wasu fusatattun matasan mazabarsa a Kano.
Rahotannin da kadaura24 ta samu sun ya cewa Kawu ya kutsa kai cikin ofishin yakin neman zaben sa, dake kan titin farm center domin boyewa magoya bayansa a jiya litinin .
Zan Murkushe Yan ta’addan kasar nan babu sassauci – Buhari
Rahotannin sun nuna cewa sanar da magoya bayan nasa Akai cewa ya sa zo ofishin nasa dake farm center.
Matasan Masu tarin yawa sun yi wa ofishin kawanya a lokacin da majalisa ke ciki tare da barazana iri iri.
bayan ya kammala abun da ake yi a cikin ofishin ya fito sai kwatsam matasan suka far masa.
Rahotanni sun tabbatar da sakin wasu mutane 3 da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
Rahotannin sun ce fusatattun magoya bayan nasa sun yi masa dirar mikiya tare da kokarin yi masa dukan tsiya amma saboda shiga tsakani da ‘yan sanda da wasu mutanen da ke kusa da shi sukai shi ne ya samu nasarar kubuta.
‘Yan sandan sun dauki lokaci mai tsawo suna kokarin fitar da shi daga harabar wurin a cikin motasarsu tare da ya ji rauni ba.
Wasu daga cikin matasan da suka fusata da suka zanta da wakilin justice watch dangane da lamarin Mai kama da wasan kwaikwayo, sun ce sun damu sosai da yadda dan Majalisar ya yi watsi da ‘yan mazabarsa kwata-kwata.
A lokacin da aka tuntubi dan majalisar domin yin karin haske kan lamarin, dan majalisar ya musanta faruwar lamarin Inda ya bayyana cewa fusatattun matasan sun je ofishinsa ne domin a sasanta a kan wani aiki da suka aiwatar wanda a karshe ya rikide zuwa rikici.
Dan majalisar wakilan ya kuma musanta yin watsi da mutanen mazabar tasa