Zabar Kashim Shattima da Tinubu yayi, ya nuna zurfin tunaninsa da kuma kishin kasar nan – Rarara

Date:

Daga Sayyadi Abubakar Sadiq

 

Shahararren mawakin Siyasar nan Alhaji Dauda Kahutu rarara ya yabawa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, bisa zabar tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Kashim Shattima a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a takarar shugaban kasa da yake yiwa jam’iyyar APC.

Dauda Kahutu rarara ya bayyana hakan ne yayin Wani taron manema labarai da ya kirawo a ofishin sa dake Kano.

Mawakin wanda shi ne shugaban kungiyar mawaka da yan fim ta 13 × 13, yace Tinubu yayi tunani sosai wajen zabo Kashim Shattima, Saboda mutum ne da yake da gogewa ta rayuwa a fannoni daban-daban musamman abun da ya shafi sha’anin tsoro.

Da yan Nigeria sun San halin da wasu kasashen suke cikin da sun godewa Allah – Buhari

“Kashim Shattima ne tsohon gwamnan ne a jihar Borno wanda ya kwashe kusan sama da Shekaru 7 yana yakar yan boko haram, don haka yasan duk ta Inda za’a bi domin a kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi al’ummar Kasar nan”. inji Shugaban 13 ×13

Yace yayi matukar mamakin yadda akai Bola Tinubu ya har yayi tunanin kawo Kashim a matsayin wanda zai yi masa mataimaki, domin duk mutane hankali su bama ya kan Kashim din Amma sai ga shi da yake Allah yana nufin jam’iyyar APC Zata ci zabe sai aka zabo Kashim.

“Babu Shakka akwai mutane da yawa da suka chanchanta a dauke su a matsayin mataimakin, Amma ko da suka ji Kashim aka dauka duk sai sukai yi Sambarka, yanzu maganar da nake yi maka duk sun taya shi murna, kuma nayi imani zasu bada duk wata gudunmawa domin APC ta sake kafa gwamnatin tarayya “

Da gaske ne Dan Kannywood Ali Artwork Madagwal ya Mutu ?

Ko da aka tambaye shi kalubalen da zasu fuskanta na hada Musulmi da Musulmi a takara sabanin sauran jam’iyyu, rarara yace harkar ba ta addini bace, akwai na bukatar waye zai iya kuma waye zai yi biyayya ba tare da an Sami matsala ba .

“Ai duk Masu maganar an hada Musulmi da Musulmi Yan jam’iyyun adawa ne da ma wadanda suke adawar Cikin gida da suka rasa Gabar kamawa sai suke maganar an hada Musulmi da Musulmi to mu yanzu a Kasar nan, kawai muna bukatar wanda zai iya ne ba tare da ala’akari da addini ko kabila ba”. Inji Rarara

Shugaban kungiyar ta 13 × 13 wanda shi ne kuma shugaban kamfanin Rarara Multimedia Nigeria Limited yace yana da kwarin gwiwar Asiwaju Bola Tinubu ne zai lashe zaben shekara ta 2023 domin bada tashi gudunmawar don cigaban Kasar nan.

Daga Karshe yayi fatan kowanne na kasar zai tabbatar ya karbi katin zabe, sannan kuma yace duk Masu karfi su taimakawa marasa karfi wajen karbar katin zaben, ta hanyar fito da akalla mutane 10 a biya musu kudin abun hawa ku kuma na Inda ake yin rijistar wato Internet Cape.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...