Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin biyan diyya ga wani gani matashi da aka sara a hannu

Date:

Daga Umar Usman Sani mainagge

 

Wata Kotun a jihar kano ta sami Wani matashi mai suna Abubakar Ayuba Dan kimanin shekaru 20 da haihuwa da laifin yiwa wani Salisu Usaini mummunan rauni wanda haka laifi ne da ya sabawa sashi na 159 na kundin Penal code.

 

Tun dai a ranar 20 ga watan maris na shekarar da muke ciki ne aka fara zargin Abubakar da dauka wata zarbadediyar wuka ya kuma kaftawa matashi Salisu Usaini a hannunsa na dama, kuma dalilin wannan aika-aikar da Abubakar din yayine ya janyo likitoci suka tabbatar da cewar babu shakka sai dai a guntilewa Salisu hannu, saboda tuni hannun ya rube.

Wata Kungiya dake goyon bayan Tinubu ta nada Aminu Nuruddeen a matsayin Daraktanta a Arewa maso Yamma

Koda likitoci suka cire hannun matashin, sai fa hannu ya cigaba da rubewa har sai da hakan ta sanya aka sake yi masa aiki, daga karshe kuma sai da aka guntile hannun gaba daya tun daga allon kafadarsa.

Aliyu Zainul Abideen shi ne ya karantawa matashin tuhumar da aike yi masa, tun kuma a wancan lokaci Abubakar ya amsa wannan zargi da aikai masa, don haka kotun ta umarci jami’an gidan gyaran Hali dasu ajiyeshi har sai anga yanayin halin da mara lafiyar yake ciki.

 

Da yake zartar masa da hukunci a ranar juma’a 15 yulin shekarar da muke ciki, Alkalin kotun shari’ar musulunci dake P.R.P Mal.Nura Yusuf Ahmad ya yankewa Mai laifin hukuncin daurin watanni 6 cikakku batare da zabin biyan tara ba, bugu da kari kuma kotun tace matashi Abubakar Ayuba zai biya ramkon kudaden da mai kara ya kashe sa’ilin da yake kwance a asibiti har naira 650,000.

 

Kotun kuma tace wajibi ne wanda akai kara ya baiwa matashi Salisu Usaini diyyar Naira Miliyan hamsin da biyu da dubu dari tara da saba’in, Alkali Nura Yusuf yace shekaru biyu kadai zai diba wajen kammala biyan wadannan kudade.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...