Daga Hauwa Umar
Wata matashiya a jihar Kano ta bude shagon bayar da hayar kayan biki da mata ke sanyawa a lokutan bukukwansu.
BBC Hausa ta rawaito Habiba Yusha’u wacce akafi sani da Beebas Glam, ta ce ta fara sana’ar ce bayan fahimtar yadda mata ke kashe kudi wajen sayan kayan tufafi yayin bikinsu wanda kuma ba su bukatar shi bayan bikin.
“Idan akayi lakari a kasar Hausa kusan duk bikin da za a yi, za ka ga amarya ta saka tufafi wanda sau daya kawai ake daura shi domin idan ta saka shi bayan biki za’a rika mata kallon mahaukaciya”.
Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin biyan diyya ga wani gani matashi da aka sara a hannu
Habiba tsohuwar mai sana’ar kwalliya ce amma a yanzu tafi mayar da hankali ne wajen bayar da hayar kayan amare lokacin bikinsu.
Kungiyar BAT dake goyon bayan Tinubu ta nada Darakta da Sakataren ta a Kano
Matashiyar ta ce akwai duk irin kayan da amarya ke bukata kuma cikin farashi mai sauki saboda ta fara sana’ar ce domin taimakawa talakawa da marayu tun da ita ma marainiya ce.