Daga Khadija Abdullahi Aliyu
A jiya da dare misalin karfe Goma sha daya na dare wani shafin Page mai suna Debit.ng hausa suka wallafa cewa jarumin nan mai shirin barkwanci kuma edita a kannywood Ali artwork wanda aka fi sani da Madagwal ya mutu .
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Allah yayiwa babban jarumi kuma mai wasan barkwanchi rasuwa A yau juma’a da misalin 11:15 na na dare bayan doguwar rashin lafiya a gadon asibiti a kwance Allah ya gafarta mishi Ameeen” yadda suka wallafa
Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin biyan diyya ga wani gani matashi da aka sara a hannu
Mutane sun yi ta nuna alhinin kan wannan labarai.
Sai dai da safiyar asabar din nan jarumin ya bayyana cikin Wani Video Inda ya bayyana cewa labarin da aka yada bashi da tushe ballantana makoma.
Yace bai dace mutane su rika shirya labarin Karya akan mutane ba, Inda yace ita mutuwa ba a karyarta idan lokaci yayi dale sai kowa ya tafi.