Kare ya ɗauki rainon marayun ƴaƴan agwagwa 15 bayan bacewar mahaifiyarsu

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya

 

A wani yanayi na tausayi da jin-ƙai, wani kare mai ban sha’awa, mai suna Fred, ya ɗauki rainon wasu marayun ƴaƴan agwagwa 15, bayan mahaifiyarsu ta ɓace ba zato ba tsammani.

 

Wani rahoto da jaridar Daily Mirror ta fitar ya baiyana cewa Fred, mai shekaru 15, ya yi suna wajen rainon dabbobi ƴan’uwansa.

 

A 2018, Fred ya game kafafen yaɗa labarai bayan da ya raini was marayun ƴaƴan agwagi guda tara da aka watsar a cikin irin wannan yanayi.

 

Shekaru bayan nan, tsohon karen ya kasance baya-goya-marayu ga ƴan’uwansa karnuka.

 

Wasu hotuna da su ka kewaye kafafen sadarwa sun nuna ƙananan ƴaƴan agwagin a durƙushe a tsakanin kafafun Fred, inda wasu kuma su ka ɗare bayansa cikin wani yanayi na shaƙatawa, yayin da suke kwance tare a rana.

 

Ƴaƴan agwagin, masu launin ɗorawa, hotonsu ya bayyana inda su ke kwance a bayan Fred wanda shi ne sabon uba a gare su.

 

Daily Nigeria ta rawaito Fred mazaunin Mountfitchet Castle ne kusa da Stansted, Essex, inda mahaifiyar ƴaƴan agwagin ta ɓace cikin dare.

 

Tun daga wannan lokacin, Fred ya ɗauki gaɓaren kula da su inda ya saɓa su a bayansa yana ɗauke da su a bayansa yana nuna su ga ma’aikata da baƙi.

 

Mai Fred, Jeremy Goldsmith, wanda kuma shi ne darekta na Dutsen Mountfitchet, ya ce bai yi mamakin cewa Fred ya sami sabbin ƴaƴa ba.

 

“A cikin shekaru 15 na mallakarsa, Fred ya shafe lokaci mai tsawo a Gidan tare da dabbobi kuma ya zama yanayi na biyu a gare shi kasancewa cikin dabbobin da aka ceto,” kamar yadda ya shaida wa Daily Mirror.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...