Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai wa ayarin motocin Shugaba Buhari hari a Katsina

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
 Wasu gungun ‘yan bindiga sun bude wuta kan ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka tura zuwa Daura, jihar Katsina gabanin zuwa Shugaban kasar domin gudanar da bukukuwan Sallah a ranar Talatar nan.
 Da yake mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar , mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya yabawa jami’an tsaron fadar shugaban kasa kan nasarar dakile harin.
 “Fadar shugaban kasa ta bayyana harin a matsayin abin bakin ciki da rashin jin dadi, lamarin harbin da ya faru a kusa da Dutsinma, jihar Katsina, a kan ayarin motocin da ke dauke da jami’an tsaro da sauran yan tawagar shugaban kasar , wadanda suka hadar da Protocol da kuma jami’an yada labarai gabanin tafiyar shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa Daura domin yin Sallah.”
 “Maharan sun bude wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton bauna amma sojoji da ‘yan sanda da jami’an DSS da ke tare da ayarin sun dakile.”
 “Mutane biyu da ke cikin ayarin motocin suna karbar magani kan kananan raunukan da suka samu.  Duk sauran ma’aikata, da ababan hawa sun isa Daura lafiya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...