Hajjin bana: Muna da kwarin gwiwar kwashe ragowar Mahajjatan Nigeria -Shugaban NAHCON

Date:

Daga Zara Jamil Isa

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta jaddada cewa tana da ƙwarin gwiwar kwashe dukkan maniyyatan da suka rage a ƙasa yayin da ake shirin rufe jigilar mahajjata zuwa Saudiyya a daren yau Lahadi.

Zuwa yanzu maniyyata fiye da 18,000 ne suke jiran a kai su Saudiyyar, yayin da hukumar ta NAHCON ta kwashe 25,361 kawai daga cikin fiye da 43,000 na alhazan Najeriya.

BBC Hausa ta rawaito cewa Daga ƙarfe 12:00 na daren yau Lahadi wa’adin rufe jigilar maniyyata zai cika, kodayake wasu kamfanonin sufurin jirage sun samu ƙarin awanni na ci gaba da aikin.

Yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Lahadi, NAHCON ta ce tana da ƙwarin gwiwar kwashe maniyyatan da suka rage zuwa ƙasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sallah: Baffa Babba ya raba buhu 2,000 na Shinkafa ga Kungiyoyin Tinubu a Kano

Babban daraktan cibiyar kula da ingantuwar aiyuka ta kasa...

Babbar Sallah : Kansilan Lajawa ya raba Naira dubu 500 ga al’ummar mazabarsa

Daga Nura Adam   Kansilan mazabar Lajawa a karamar hukumar Wudil...

Da dumi-dumi: Kotu ta aike da Matashin dake shigar mata a Tiktok da film gidan gyari

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i...