An yi jana’izar Nura Mustapha Waye, daraktan fim in Izzar So mai dogon zango da ake nunawa a dandalin Youtube.
An gudanar da jana’izar ce a unguwarsu ta Goron Dutse da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.
Sanarwar rasuwarsa a safiyar yau Lahadi ta bai wa mutane mamaki saboda ba a san shi da wata rashin lafiya ba kuma lafiya kalau aka rabu da shi, kamar yadda makusantansa suka bayyana.
Nura ya kasance daraktan fina-finai da dama ciki har da Izzar So, wanda ke jan hankalin masu kallo musamman matasa a shafukan sada zumunta.
Tuni wasu daga cikin taurarin Kannywood suka yi ta’aziyya ga Nura, suna mai bayyana shi a matsayin mutumin kirki.