Shirin KANO CARES ya tallafawa Masu karamin karfi guda 1000 da kayan Noma

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Shirin tallafawa masu karamin karfi wadanda annobar corona ta tagayyara tattalin arzikinsu wato KANO CARES project ya raba kayan noma da kadarori ga masu karamin karfi da marasa galihu 1000 a jihar Kano.

 

Jami’in kula da ayyukan shirin a jihar Kano Malam Rufa’I Halilu ya bayyana haka a lokacin mika kayayyakin ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a jihar, inda ya bayyana cewa shirin yana amfani da tsarin ci gaban al’umma (CDD) wanda ke ba da dama ga al’umma domin inganta musu.

 

Rufa’I ya ce rabon kayayyakin ya zo a dai-dai lokaci da ya dace musamman a yanzu da wasu manoma suka fara shuka a yankunansu.

 

A sanarwar da jami’ar yada labaran shirin a kano Shafa’atu Sa’id Karaye ta aikowa kadaura24 ta ce Rufa’i ya tabbatar da cewa Kano CARES za ta ci gaba da sanya farin ciki a fuskokin mabukata ta hanyar basu tallafin da zasu dogara da shi don bunkasa tattalin arziki su.

 

Ya yi nuni da cewa, aikin na Kano CARES na samun tallafin Bankin Duniya da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar kano kuma an yi shi ne domin masu karamin karfi da marasa galihu a cikin al’umma musamman wadanda annobar cutar covid19 ta tagayyara.

 

 “Mun kai kayayyakin noma da kadarori ga kananan hukumomin Munjibir, Makoda, Shanono, Bagwai, Rano, Sumaila, Albasu, Gaya, Kiru da Doguwa.” Inji Rufa’i Halilu

 “Covid 19 ta shafi rayuwar mutane da dama ta fannin tattalin arziki kuma ta sauya rayuwarsu ta yadda wasu ke dogaro da Naira 500 kacal a kowace rana.” Inji shi

 

Rufa’I ya bayyana cewa daga cikin kananan hukumomi 44 da shirin na Kano CARES zai shiga, 10 sun ci gajiyar tallafin noma da kadarori daban-daban “wadanda suka hada da ingantattun iri, maganin kwari, maganin ciyawa, yayin da kadarori na noman suka hada da kayan shuka, abubuwan feshi, injina da dai sauransu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...