Daga Auwal Alhassan Kademi
A yayin da ake jigilar maniyata aikin Hajji bana daga jihar Katsina zuwa kasa mai tsarkin wata mata ta kunna kai cikin jirgin don tafiya kasa mai tsarki ba tare da ta biya ko sin Kobo ba.
ita dai wannan mata mai suna Halimas Sadiya tace kunna kai cikin jirgin ne lokacin da ake tsaka da dibar rukuni na 3 na Maniyatan jihar a ranar alhamis a filin jirgin sama ba tunawa da Umaru Musa Yar adu’a.
Kadaura24 ta rawaito a bayanin da Halima ta yiwa manema labarai ta ce bata da kowacce irin takarar ta zuwa saudiyya, Amma ta rika wuce wurare da dama har ta kai ga ta shiga motar da aka dauko maniyatan zuwa filin jirgi Inda anan ne jami’an tsaro suka kama Halima lokacin da take kokarin shiga jirgi don tafiya kasa mai tsarki don sauke farali.
” Tun lokacin da naje aikin Hajji na farko kullum hankali na yana chan Ina son sake komawa saboda in sake yin aikin Hajji, shi yasa na yanke a Raina cewa bana zan sake komawa saudiyya duk da bani da kudi”. inji Halima
Ta kara da cewa tuni ta yi sallama da ‘ya’yan ta da sauran yan uwanta kuma duk ta sanar da su cewa an kirawo su domin tafiya aikin hajji kamar yadda aka sanar a Radio.
Halima dai yanzu haka tana hannun jami’an tsaro domin amsa tambayoyi ,sai dai ta yi roko ga Alhaji Dahiru Mangal da cewa ya taimaka mata da kujerar aikin hajji domin ta cika burinta na sake komawa kasa mai tsarkin.