Daga Isa Ahmad Getso
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC ta jihar Kano sun nada Ibrahim Maishinku tafarkin alkhairi a matsayin shugaban riko na kungiyar APC Media forum ta jihar nan.
Kwamitin rikon dai an samar da shi ne domin ya shirya zaben sabbin shugabannin kungiyar wadanda wa’adin su ya kare tun a ranar alhamis 30 ga watan Yunin da ya gabata.
An dorawa kwamitin su Maishinkun nauyin shiryawa da gudanar da zabe tare da mika ragamar tafiyar da harkokin kungiyar ga sabbin shugabannin da za’a zaba.
A baya dai an Sha dambarwa kan waye ya kamata ya zama shugabannin kungiyar, hakan kuma yayi sanadiyar samun rabuwar kan ‘ya’yan kungiyar Inda wasu sukai biyayya ga tsagin Sale Kala Kawo da kuma tsagin Su Ibrahim Falke.
A zantawarsa da wakilin kadaura24 shugaban kwamitin rikon ya bada tabbacin zasu shirya nagartacce kuma ingantaccen zabe wanda kowa Zai yi alfahari da shi akan lokacin da aka dibarwa kwamitin .
” Tun da aka bamu wannan raga tuni mun fara aikin da aka dora mana, Inda muke sa ran zamu fara sayar da fom din tsayawa takarar mukamin shugabanci a kungiyar ta APC Media Forum”. Inji Maishinku
Yace za’a sayar da fom din takarar shugaba akan kudi Naira Dubu dari, sai sakatare akan kudi Naira Dubu 50, Ma’aji Woman Leader da PRO Naira Dubu 30 sauran mukaman kuma Naira Dubu 20, kujerar Masu bukatar ta musamman kuma Naira Dubu 20.
Ya yi fatan dukkanin ‘ya’yan kungiyar da sauran masu ruwa da tsaki n Jam’iyyar su ba su hadin kai don samun nasarar da suke fata.