Daga Shehu Sulaiman Sharfadi
Kungiyar kasuwar hada hadar wayoyinhannu dake farm centre tasha alwashin hada hannu da bankuna domin samarwa yayan kungiyar rancen jari domin bunkasar tattalin arzikin kasuwar.
Shugaban Kungiyar Alhaji Hassan Abubakar Abdullahi ne ya sanar da hakan a zantawarsa da wakilin kadaura24 a ofishinsa dake nan kano.
Alhaji Hassan ya bayyana cewar sun gayyato bankuna sun zauna da su domin baiwa ‘ya’yan kungiyar rancen, don su inganta jarinsu domin cigaban kasuwanci a kasuwar da jihar kano dama kasa baki daya.
Yace bankuna da zasu yi mu’amalar da su sun hadar da Wema bank,Unity bank, Sterling bank da dai sauran bankuna da dama don bunkasar tattalin arzikin kasuwar.
Shugaban ya yabawa ya’yan kungiyar bisa nuna kishin su kan yadda zasu dogara da kansu da kuma hadin kai da goyon baya dari bisa dari da suke baiwa shugabannin kungiyar don ciyar da kasuwar gaba.
Dangane da sha’anin tsaro kuwa Alhaji Hassan ya yabawa Kwamatin tsaro da hukumomin tsaro a kasuwar bisa yadda suke aiki tukuru wajen tsaftace kasuwar daga batagari masu saye da sayar da wayoyi da naura mai kwakwalwa na sata.
Kazalika ya bayyana cewar kasuwar su ta lashe gasar tsafta kasuwanni ta karshe wata da gwamnati ke gudanarwa, saboda irin tsayuwar dakan da sukai na ganin an raba kasuwar daga datti, don ingata muhalli da lafiya Masu shiga kasuwar ta farm center.
Daga karshe ya yi kira ga gwamnati kan ta taimaka ta cike ramukan dake kan titinan kasuwar domin saukakawa ababen hawa dake shige da fice a kasuwar.