Daga Abdulrashid B Imam
Shawarar da gwamnatin Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta yanke ta bai wa dukkan mazauna Jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane ta jawo ce-ce–ku-ce a kasar.
Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji kuma hakan zai ba mutane musamman manoma damar kare kawunansu a lokaci da suke gudanar da ayyukansu.
“Hare-haren ta’addanci sun kasance abin damuwa ga jama’a da gwamnatin jiha. Don haka ne, domin mu magance wannan matsala baki daya a yankunanmu, gwamnati ba ta da
zabin da ya wuce daukar matakan da suka hada da bai wa mutane damar shiryawa da kuma mallakar bindigogi domin kare kansu daga ‘yan fashin daji,” in ji sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya fitar ranar Asabar.
Ta kara da cewa gwamnati ta umarci Kwamishinan ‘yan sanda ya bai wa dukkan mutanen da suka dace da kuma suke bukatar mallakar bindiga su mallake ta domin kare kansu.
Gwamnatin Zamfara ta dauki matakin ne watanni da dama bayan gwamnatin Jihar Katsina da ke makwabtaka da kuma Binuwai da ke Tsakiyar kasar sun umarci mazauna jihar su mallaki bindiga domin kare kansu daga masu kai hare-hare.
Sai dai masu sharhi kan sha’anin tsaro irin su Barista Audu Bulama Bukari suna ganin kyale farar-hula su mallaki bindiga yana da matukar hadari.
Arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane, lamarin da ya sa jama’a da dama a jihohin da ke wannan yankin suka soma yanke ƙauna ga jami’an tsaron ƙasar.
Me dokar Najeriya ta ce kan mallakar bindiga?
BBC ta tuntuɓi Barrista Abubakar El Zubair, wani fitaccen lauya a birnin Kaduna, wanda ke cewa dokar Najeriya ba ta yarda mutum ya mallaki bindiga ba sai dai idan bindigar ta farauta ce.
Ya ce idan za a ce ƴan Najeriya su mallaki bindiga kamar sauran ƙasashe irin su Amurka, sai majalisar tarayya ta yi sabuwar doka sa’annan ta yi muhawara a kanta daga nan shugaban ƙasa ya sa hannu ta zama doka.
“To amma idan ba a bi waɗannan matakan ba, a tsarin da ake ciki a yanzu, babu wanda yake da damar ya mallaki bindiga sai idan na farauta ne, ita ma ta farautar akwai yadda ake yi a mallaka,” in ji Barrista El Zubair.
Waɗanne matakai mutum zai bi idan zai mallaki bindigar farauta.
Wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma shugaban kamfanin Beacon Consulting Group, Malam Kabiru Adamu, ya bayyana cewa a tsarin dokar Najeriya mutum biyu ne ke da ikon bayar da lasisin bindiga – shugaban ƙasa da babban sufeton ƴan sanda wanda shugaban ƙasar ya ba wakilcin bayar da lasisin.
“A ƙarƙashin dokar akwai ƙa’idoji da yawa wadanda shi babban sufeton ƴan sanda ya kamata ya bi don ya tabbatar da cewa shi wanda aka ba makamin nan mutumi ne na ƙwarai kuma yana bin doƙar ƙasa,” in ji Malam Kabiru Adamu.
BBC ta duba sashen makamai na Najeriya wanda ya yi bayani kan sharuɗɗan mallakar bindiga irin wadda doka ta amince ƴan ƙasa su mallaka:
Dole ne wanda zai mallaki bindiga ya kasance mutum ne mai cikakken hankali, kuma a gwada ƙwaƙwalwarsa a san cewa an gamsu da yanayin tunaninsa
Wanda ke son ya mallaki bindiga dole ne sai ya kai shekara 18
Dole ne a tabbatar da mutum ba shi da matsalar ido ko kuma mutum ba shi da larurar makanta
Haka kuma sai an tabbatar da mutum ba shi da saurin fushi
Sai an tabbatar da cewa cikin shekara biyar da suka wuce ba a kama mutum da wani laifi ba.
Sai dai a cewar Malam Kabiru Adamu, a lokutan baya sufeto janar na ƴan sanda da aka yi a baya sun sha dakatar da bayar da lasisin bindiga saboda wasu dalilai.
“A baya mun so mu bincika mu ga lasisi nawa aka bayar kuma makamai nawa ne ke hannun ƴan ƙasa kuma a gaskiya mun gano babu wani kundi da zai nuna yawan lasisin da aka bayar, a tunanina gudun kada abin ya ɓaci sai aka dakatar da bayar da lasisin.
“Yanzu dai a sani na a halin da ake ciki an daina bayar da wannan lasisin duk da yake akwai hanyoyin da ake bi ta bayan fage wanda misali wasu ƴan sanda saboda wasu dalilai nasu za su iya tuntuɓar mutum su ce ya kawo kuɗaɗe za su ba shi lasisi, amma dai a takaice an dakatar da bayar da lasisi a sani na tun lokacin mulkin Goodluck Jonathan,” in ji Malam Kabiru Adamu