Hajjin bana: Hukumar NAHCON ta koka da Rashin samun karin kujerun aikin Hajji daga Saudiyya

Date:

Daga Zara Jamil Isa

 

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta bayyana cewa duk da kokarin da Najeriya ta yi, don samin karin kujerun aikin Hajjin bana abun ya ci tura.

 

Har ila yau, NAHCON ta ce kokarin diflomasiyya da tayi don a bar jami’an da suka haura shekaru 65 su je Saudiyya don taimakawa alhazai a yayin aikin Hajjin bana.

 

Kakakin Hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa data sanyawa hannu a ranar Talata, inda ta ce Saudiyya ta ki amincewa da bukatar.

 

Hukumomin Saudiyya sun ware sama da kujeru 43,000 ga maniyatan Najeriya a bana, tun bayan shafe shekaru biyu ba  tare da an baiwa kasashe izini ba shiga kasar ba.

NAHCON ta raba kason da aka bata ga daukacin jihohin kasar nan 36 da babban birnin tarayya Abuja da dakarun soji da kuma yan jirgin yawo, lamarin da ya haifar da rikici a tsakanin kungiyoyin da NAHCON. hukumar ta bukaci karin kujeru 5000 daga ma’aikatar Hajji da Umrah domin magance matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yansanda sun Haramta Hawan Sallah a Kano

Daga Abdulmajid Habib   Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta...

Sanata Barau ya kai ziyarar jaje ga iyalan ‘yan wasan da suka rasu, ya bayar da gudunmuwar N22m

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin, a...

Hawan sallah : Sarki Sanusi ya umarci hakimai su shigo cikin birnin Kano

Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata takarda mai...

Yadda kamfanin ganyen shayi na Z&Y ke fuskantar matsin lamba daga TOP TEAA

Wani matashin ɗan kasuwa daga jihar Kano, mai suna...