Daga Auwal Alhassan Kademi
A yau Litinin ne ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rantsar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin alkalin alkalan Najeriya (CJN).
Hakan ya biyo bayan murabus din mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad bisa dalilan lafiya.
Mai shari’a Ariwoola, wanda shi ne babban alkalin kotun koli, za a rantsar da shi da misalin karfe biyu na rana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Majiyoyi sun ce zai yi aiki a matsayin alkalin alkalai har zuwa lokacin da shugaban kasa zai mika sunansa ga majalisar dattawa domin tabbatar da shi a matsayin babban alkalin alkalan Najeriya (CJN).
An haife shi a ranar 22 ga watan Agustan 1954, Mai shari’a Ariwoola dan jihar Oyo ne, ya taba zama mai shari’a na kotun daukaka kara kafin daga bisani a daukaka shi zuwa kotun koli a shekarar 2011.