IPMAN ta ce ba zasu sayar da man fetur kasa da Naira 180

Date:

Kungiyar masu dillancin man fetur a Najeriya ta ce ta fara sayar da duk lita daya ta mai tsakanin N170 zuwa N190 tana mai cewa abu ne mai wahala su iya ci gaba da sayar da shi kan naira 165.

Jaridar The Nation ta ambato Sakataren IPMAN reshen Legas Akeem Balogun na cewa ”lura da yadda kasuwar take a yanzu, babu yadda za a yi mu sayar da mai kasa da naira 180 a duk lita”.

Ya kara da cewa ”duk wani mamba da wata hukuma ta hana yin haka ya yi gaggawar sanar da uwar kungiya.”

An shafe watanni ana wahalar mai a Najeriya, musamman a manyan biranen kasar da suka hada da Abuja da Lagos.

IPMAN reshen na jihar Legas, ta ce rufe gidajen man wasu mambobinta ya kara haifar da dogayen layuka musamman a Lagos da Akure da Ado-Ekiti da Abeokuta da Jos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya Naɗa Ahmed Musa a Matsayin Darakta Janar na Kano Pillars

Daga Zakaria Adam Jigirya   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...