Tsohon Ministan Neje Delta Orubebe ya fice daga jam’iyyar PDP

Date:

Daga Sadiya Muhd Sabo

Tsohon ministan ma’aikatar kula da Harkokin Neja Delta a Najeriya Godsday Orubebe ya sanar da barin jam’iyyar adawa ta PDP.

Orubebe ya sanar da ficewar ne a wasikar da ya aike wa Shugaban jam’iyyar PDPn Iyorchia Ayu, in ji jaridar TheCable.

”Na zaci a lokacin da muka sha kaye a zaben shugaban kasa a 2015 a wani yanayi mai sarkakiya, jam’iyyar za ta yi amfani da lokacin da take da shi na zamanta babbar jam’iyyar adawa ta lalubo hanyoyin dawowa kan mulki”, in ji Orubebe.

Talla

A cewar Mr Orubebe halin da PDP take ciki a halin yanzu ya nuna cewa jam’iyyar ba ta shirya cin zaben 2023 ba.

Sunan tsohon ministan ya karade shafukan sada zumunta a lokacin zaben 2015, a lokacin da ya kasa ya tsare a zauren bayyana sakamakon zabe, yana ikirarin cewa INEC ba ta shirya yi wa PDP adalci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sallah: Baffa Babba ya raba buhu 2,000 na Shinkafa ga Kungiyoyin Tinubu a Kano

Babban daraktan cibiyar kula da ingantuwar aiyuka ta kasa...

Babbar Sallah : Kansilan Lajawa ya raba Naira dubu 500 ga al’ummar mazabarsa

Daga Nura Adam   Kansilan mazabar Lajawa a karamar hukumar Wudil...

Da dumi-dumi: Kotu ta aike da Matashin dake shigar mata a Tiktok da film gidan gyari

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i...