Daga Kamal Yahya Zakaria
A shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji na shekarar 1443, Masarautar Saudi Arabia ta sanar da isowar wani jirgin ruwa dauke da dabbobi ta tashar ruwa ta kasar mai tsarkin dake Jeddah.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Tumaki 50,000, ne suka isa kasar daga Nahiyar Africa Wadanda alhazai zasu yi amfani da su wajen hadaya wanda kuma aka mai da shi dole ga kowanne mahajjaci.
Kadaura24 ta rawaito hukumomin kasa mai tsarki sun tabbatar da fito da sabbin tsare-tsare a aikin Hajji bana.