Daga Auwal Alhassan Kademi
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin shugaban hukumar kula kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA), Baffa Babba Dan Agundi a matsayin mukaddashin manajan darakta na hukumar kula da hakkin mai saya da mai sayarwa ta jihar Kano (KSCPC), har a nada babban manajan darakta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan kano Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Sanarwar ta ce nadin na Baffa Babba ya fara aiki ne nan take, kuma an bashi damar kula da dukkanin al’amuran hukumar har zuwa lokacin da za’a nada babban Manajan Darakta hukumar.