Daga Zara Jamil Isa
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta bada tabbacin cewa kamfanin jirgin sama na Max air ne zai yi jigilar maniyatan jihar nan zuwa kasa mai tsarki.
Kadaura24 ta rawaito Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Muhd Abba Danbatta ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kano.
Alhaji Muhd Abba Danbatta yace sun kammala tattauanawa da hukumar kula da aikin Hajji ta kasa Nahcon inda suka tsayar da matsayar kamfanin jirgin sama na Max air shi ne zai yi jigilar maniyatan jihar Kano zuwa kasa mai tsarki.
Yace dama rashin kammala tattauanawa da hukumar Nahcon ne ya hana hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta sanar da kamfanin da zai yi jigilar maniyatan jihar.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa hukumar jin dadin alhazai ta kano taki amincewa da kamfanin jirgin na Azman saboda da wasu dalilai.
Babban sakataren ya kuma ce zasu fara tantance lafiya maniyatan su a gobe litinin domin tabbatar da cewa ba’a sami alhazai masu dauke da cutar murar burrai da cutar corona ba.
Ya bada tabbacin kowanne lokaci daga yanzu za’a fara jigilar maniyatan jihar Kano zuwa kasa mai tsarki.