Daga Zara Jamil Isa
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta bayyana cewa har yanzu tana tattaunawa da hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON kan kamfanin jirgin da zai jigilar alhazan jihar zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Kadaura24 ta ruwaito cewa an samu cece-kuce bayan NAHCON ta sanya Kano cikin jihohin da kamfanin Azman zai yi jigilar maniyyatasu zuwa kasa mai tsarki a lokacin aikin Hajjin bana.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun ce hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ki amincewa da kamfanin Azman Air a matsayin jirgin da zai yi jigilar maniyyata.
Sai dai babban sakataren hukumar Muhammad Abba Dambatta, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Asabar din nan, ya ce batun kin amincewa da kamfanin bai taso ba, domin tun farko hukumar ba ta taba rubutawa kamfanin Azman takarar aiki ba ko kamfanin ya rubutowa hukumar.
Dambatta ya ce hukumar na ci gaba da tattaunawa da NAHCON kan kamfanin jirgin sama domin jigilar maniyyatan jihar Kano.
Babban sakataren ya kara da cewa nan da sa’o’i 24 masu zuwa za a fitar da sanarwar kan jirgin da za’a yi amfani da shi wajen jigilar maniyyatan jihar.
“Muna tattaunawa da hukumar NAHCON kan kamfanin jirgin sama domin jigilar Alhazan jihar Kano. A kowane lokaci daga yanzu zuwa gobe, za mu bayyana matsayarmu”
“Amma, mun shirya 100 bisa 100 don fara jigilar maniyatan mu kowanne lokaci da yanzu. Muna tattaunawa da NAHCON, ciki har da shugaban kwamitin sufurin jiragen sama , kwamishinan ayyuka da shugaban NAHCON, don hakan nan ba da jimawa ba za mu bayyana matsayarmu”.
“Ina son tabbatar muku cewa, a shirye muke mu fara jigilar Ko da an da awowi biyu ne zamu kirawo maniyyatan mu don haka mu a shirye muke,” in ji Dambatta.
Sakataren zartarwa ya sanar da cewa maniyyatan jihar za su biya N2, 449, 607.89 daga cikin N2, 500, 000 da suka ajiye.
Ya kara da cewa dukkan maniyyatan da suka biya Naira Miliyan biyu da dubu dari biyar za’a Maida musi da abun da ya rage na kudadensu ta asusun ajiyarsu na bankunansu
Ya jaddada cewa hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta kammala shirye-shiryenta kuma a shirye take domin gudanar da aikin Hajjin da za’a sami nasara a cikin sa.