Daga Auwal Alhassan Kademi
Jam’iyyar NNPP, ta kalubalanci bukatar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na neman rancen Naira biliyan 10 daga bankin Access don sanya na’urorin daukar hoto na CCTV a jihar.
Jam’iyyar NNPP ba za ta zuba Ido tana kallon wannan gwamnati tana tarawa jihar kano basussuka ba, ba tare da ganin aiyuka a fili ba.
Cikin sanarwar da shugaban jam’iyyar NNPP na jihar kano Umar Haruna doguwa ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24 yace ga dukkan alamu Gwamna Ganduje yana amfani da kujerarsa wajen jingina makomar jihar da ta yaran mu.
Sanarwar ta kara da cewa Sakamakon gazawar gwamnan na biyan kudin jarrabawa ga daliban sakandire, dalibai da dama ne aka tilastawa barin makaranta a lokacin da wasu daliban ke gaba da kammala makarantu.
“Yayin da jihar ke fama da matsalar karancin ruwa, amma gwamnan ya zabi ya ci bashi don yin aikin da bai kai ruwa muhimmanci ba”.
Umar Haruna Doguwa ya ce jam’iyyar NNPP na kira ga majalisar dokokin jihar kano da su daina barin irin wadannan bukatun suna wucewa ba.