Gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da cewa idan bukatar sake toshe layukan sadarwa ta taso za a aiwatar da hakan ba tare da wani bata lokaci ba.
Gwamna Matawalle ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yana musanta rade-radin da ake yi cewa za a rufe layukan sadarwa a Zamfara a karo na biyu.
Sanarwar dauke da sa hannun mataimaki na musamman ga Gwamna Matawalle ya fitar, Zailani Bappa, na cewa duk da cewa kawo yanzu babu wannan maganar a kasar, kamar yadda ake yada jita-jita, akwai yiwuwar faruwar hakan idan bukatar ta taso.
Sannan ta jadada cewa gwamna Matawalle ya damu matuka da matsalolin tsaron jihar, kuma ya na cikin damuwa saboda halin da ‘yan bindiga ke jefa al’ummar jihar.
A baya dai gwamnati ta dau irin wannan mataki, lokacin da hare-hare da satar mutane domin neman kudin fansa ya kazance a jihar ta Zamfara.