An fara kiraye-kirayen a sauke shugaban APC na kasa Abdullahi Adamu daga mukaminsa

Date:

Wani rikici ya barke a shalkwatar jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da ke Abuja a ranar Alhamis.

Wasu matasa masu zanga-zanga sun hallara a ofishin jam’iyyar inda rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ke cewa masu zanga-zangar sun rika yin wakoki suna sukar shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu.

rahoton ya ce matasan sun fito daga jihar Kogi ne, kuma sun isa shalkwatar ne yayin da jam’iyyar ke wani taro.

Masu zanga-zangar na nuna bacin ransu ne kan abin da suka kira “kwace tikitin takarar mukamin dan majalisar wakilai da aka yi wa wani gwamninsu” kuma aka mika shi ga wani mutumin na daban.

Jami’an tsaro sun kulle kofofin babban ofishin jam’iyyar yayin da suka ji masu zanga-zangar na ikirarin hana Abdullahi Adamu ficewa daga ginin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...