Daga Shehu Sulaiman Sharfadi
Wani Dan rajin cigaban matasa Isa Umar ya yi kira ga daukacin matasan jihar kano da su yi kokari su mallaki katin zabe duba da cewar shi ne kadai abin da dan kasa zai kare yancinsa wajen zabar shugabanin nagari a zaben shekara ta 2023.
Isa Umar Zaura wanda guda ne cikin jagororin tafiyar siyasar gidan A.A Zauna ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin Kadaura24 a Kano.
Jagoran ya bayyana cewar shekaru 22 bayan dawowa mulkin demokaradiyya mafi akasarin matasan wasunsu suna da shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai don haka ya zama wajibi agaresu su mallaki Katin zabe don zabar shugabanni nagari a zaben shekara ta 2023.
Alhaji Isa ya kuma bukaci matasan su rungumi sana’o’i komai kankantarsu don kare mutuncinsu da kuma kaucewa fadawa hannun batagari wadandaKeyin amfani dasu don biyan bukatun kansu musamman ma duba da karatowar zaben shekarar 2023.
Daga karshe yayi kira ga al’ummar kasar nan da su tabbata da cewa sun duba cancanta yayin zaben shugabanni da kuma yin addu’ar Allah ya zabawa jihar Kano dama kasa baki daya shugabanni nagari.