Daga Rukayya Abdullahi Maida
Tsohon Dan majalisa mai wakiltar kiru da Bebeji a Majalisar wakilai Abdulmumin jibril Kofo , ya kaddamar da kasuwar manoma da cibiyar kasuwanci ta kofa domin bunkasa harkar noma da kasuwanci, a Karamar hukumar Bebeji Dake Nan Kano.
Tsohon Dan majalisar wanda yanzu shi ne dan takarar Kiru da Bebeji a Majalisar wakilai cikin jam’iyyar NNPP a zabe mai zuwa ya gina
Katafariyar kasuwar irinta ta farko a Kano wadda aka kwashe Shekaru goma ana aikinta zata zamo wata hanya ta bunkasa harkokin noma da Kasuwanci da Kuma samarwa matasa aikin yi a kano.
Kasuwar mai dauke da shaguna guda dari biyu, da masallaci Mai daukar masallata dubu biyar da gidan Mai, da Kuma Babban filin Ajiye manyan motocin tirela- tirela masu daukar kaya da Ajiyewa sama da guda dari.
Da yake yiwa Manema labarai Karin haske game da Kasuwar Abdulmumini kofa ya bayyana cewa kasuwar kasuwa ce da duk abinda ake nema za’a samu, kama daga dakin Hutu, wurin karbar magani, sannan Kuma sun shirya tsaf wajen bada tsaro Mai inganci a wannan kasuwa.
Ya Kara da cewa yanzu haka ma’aikata sama da dari biyar ke aiki tukuru a wannan kasuwar Kuma duk da Haka ana sa ran za’a Kara daukar wasu baya ga Waɗanda zasu yi dakon kaya da yaran shago da dai Sauransu.
” Nan gaba za’a sake daukar ma’aikata sama da dari biyu a Saka musu Albashi don rage matasa masu zaman banza da Kuma inganta Rayuwar su”.
Anasa jawabin shugaban Yan kasuwa na kasa Dakta Bature Abdulaziz ya yabawa tsohon Dan majalisar bisa wannan namijin kokari da yayi, Wanda yace ya halacci bude kasuwanni da dama Amma bai ga Kasuwar da akai mata tsari irin wannan ba.
“Aikin gina irin wannan Kasuwa da kofa yayi ya nuna tsantsar kishinsa ga al’ummar kofa Kano da Nigeria baki daya, Saboda Allah ne kadai yasan wadanda zasu sami arziki a Kasuwar”.
“Kofa ya cika cikkaken dan kishin kasa Kuma dan siyasar da yakamata yazama abin koyi ga Yan uwansa yan Siyasa, kasancewar yadda ya nemo kudinsa Kuma ya kashesu a mahaifarsa da Abubuwa na cigaban Al’umma baki daya”. Inji Danbature
Shi kuwa Shugaban kasuwar kayan Abinci dake Dawanau Alh. Murtala Isa cewa yayi sunyi farin ciki da wannan kasuwa da tazo da kyakkyawan tsari, Kuma kasuwar Dawanau zatayi alfari da wannan kasuwa,
Daga karshe yayi masa fatan Alkhairi da fatan masu hannu da shuni da yan Siyasa zasu yi koyi da wannan aikin Alkhairi da cigaban kasa.
Taron ya samu halartar manyan mutane, Yan siyasa da suka hadar da Shugaban Majalisar wakilai femi Gbejibiamila da dan takardar Gwamna a jam’iyyar NNPP Abba kabiru Yusuf, da shugaban majalisar malamai Sheikh Abdullahi Pakistan Wanda ya jagoranci sallah juma’a a katafaren masallacin Dake cikin kasuwar ta manoma da cibiyar kasuwanci ta kofa Wanda Abdulmumini kofa ya sadaukar ga mahaiginsa.