Daga Zaiyad Isama’il
Kungiyar Nyako support Group a jihar Adamawa ta jadda anniyarta na marawa Sen Abdulaziz M Nyako da sauran yan takarkarun jam’iyar Apc goyon baya a zaben gama gari na shekaran 2023.
Shugaban kungiyan Jibrilla Muhammad ne ya shaida hakan a sa’ilin taron masu ruwa da saki dama yayan kungiyar a fadin jihar Adamawa, wanda ya gudana a dakin taro dake gidan Nyako a Yola.
A cewarsa dai manufar taron shine domin zaburar da membobin kungiyar tare da hadinkan a sakain su ne yasa akayi taro.
Dayake sokacin kan chancantar takaran Sen. Aziz Nyako Muhammad ya bukaci membobin kungiyar da su baiwa senatan goyon baya da dukkan yan takarkarun jam’iyar Apc a fadin jihar goyon baya I zuwa ga maci.
Shima sakataren kungiyar ya bukaci da shuwagabanin kungiya da su kara fada aikace-aikacen kungiya a dukkan lungu da sakon jihar dama kasa baki daya.
Acewarsa yin hakan zai kara daga darajan kungiyar a idon duniya.
Tun farko a jawabin da yayi sekataran tsare-tsaren kungiya Malam Maikano Gwalam yabada taikaiceccen tarihin kafuwar kungiyar, indama ya bukaci membobin kungiyar da su kara zage dantse kan manufofin kungiyar.
A jawabin da sukayi shugaban kungiyar Apc National Youth Vanguard da ma comrd Mohammed Adamu duk sun bukacin jagororin kungiyar Nyako support group da su kara azama kan kare mutunci tsohon Gomna Jihar Murtala H. Nyako dama zuriyarsa.
Daga bisani an rantsar da shuwagabanin kungiyar a matakin kanana hukumomi dama wasu dade daden mukamai wanda shugaban kungiyar yayi