SHUGABAN K/H SUMAILA KA IYA KAWOWA KANO MATSALAR TSARO — RIMI YOUTH AWARENESS

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Kungiyar da ke rajin cigaban yankin Rimi a Karamar hukumar Sumaila wato “Rimi Youth Awareness” ta zargi shugaban Karamar hukumar da goyon bayan matasan yankin da suka kware wajen shaye-shaye da fadan daba wanda hakan ke zama barazana ga tsaron yankin.

Shugaban kungiyar Abba Munkaila Yahaya ne ya bayyana hakan a lokacin da ‘ya’yan kungiyar suka ziyarci gidan Radio Tarayya Pyramid FM Kano.

Kungiyar ta yi zargin cewa shugaban Karamar hukumar ta Sumaila Honarabil Ibrahim Hamisu Rimi yayi amfani da wani Fili da ya kasance ragowar filin masallacin juma’a wajen ginawa ‘yan shaye-shaye rumfa wacce ta kasance matattaran aikata ba dai-dai ba a yankin.

Ya cigaba da cewa sun ziyarci dukkan masu ruwa da tsaki domin kawo karshen ayyukan ‘yan shaye-shayen wanda suke fadace-fadace a yankin da aikata ayyukan da basu da ce ba amma sun gaya musu cewa masu ruwa da tsaki wanda suka fi karfinsu ne ke goyon bayan su.

‘Yan kungiyar sun bayyana cewa Karamar hukumar Sumaila ta na daya daga cikin kanana hukumomin jihar Kano dake fama da matsalar satar mutane domin neman kudin fansa nan-da-can wanda suke tsoron kada a rika amfani da wadancan bata gari wajen aikata munanan ayyuka ciki harda garkuwa da mutane da kashe-kashe da sauran ayyukan ashsha.

“Babban abin da muke tsoro, wannan gurin zai iya zama kafa ko mafaka ta ‘yan ta-da kayar ba da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa domin yankin yana kusa da jejin da ake yawan kama masu satar mutane, kuma shaye-shayen ya kai ga cewa yara nayi, matasa na yi, manya ma nayi to abin da zai faru a nan gaba muke tsoro” inji Abba Munkaila.

Ya ce “muna Kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa (Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano da hukumar hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA) da sauran hukumomin da abin ya shafa da su kawowa mana dauki domin ganin wannan rumfa an tasheta daga wannan guri domin tsira da mutuncinmu da na yaran mu”.

Runfar a tsakiyar gari ta ke jikin babban masallacin juma’a na garin rimin Sumaila kuma bata wuce watanni hudu ko biyar ba amma ta gallabi kowa da dukkanin al’ummar yankin” inji shi.

“Mun tuntubi dukkanin masu ruwa da tsaki kama daga Mai unguwa da Dagaci da harma da hakimi kuma kowa yayi iyakar abin da zai iya amma abin ya ci tura, munyi kokarin mu samu shugaban Karamar hukumar amma abin ya ci tura” inji Abba.

‘ya’yan kungiyar daga nan sunyi yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kai musu dauki domin masalahar al’ummar yankin.

To amma shugaban karamar hukumar ta Sumaila Honarabil Ibrahim Hamisu Rimi bai amsa kiraye-kirayen da wakilinmu yayi masa ba, bai kuma mayar da martanin sakon karta kwana da aka aika masa ta wayar salular sa ba har zuwa hada wannan rahoto.

To amma zamu cigaba da bibiya.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin manyan ‘yan siyasa da masu rike da manyan mukamai ke gudun zama a yankunan karamar hukumar ta Sumaila da suka hadar da Gani da Dagora da Rimi da kuma Massu domin gudun abin da kaje ya zo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...