Daga Rukayya Abdullahi Maida
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano dake Wudil KUST da Suna Aliko Dangote
Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce ci gaban ya biyo bayan shawarar da kwamitin da aka tura jami’ar ya bayar.
Ya bayyana cewa a yanzu za’a rika kiran makarantar da Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUST), Wudil.
Malam Garba ya kara da cewa an mika batun ga majalisar dokokin jihar domin nazarin dokokin da suka kafa jami’ar domin yin gyara.