Daga Mubaraka Aliyu Ibrahim
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya tafi kasa mai tsarki domin gudanar da ibadar Umarah a saboda haka ne ya mika ragamar Mulkin Kano ga Mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.
Hakan na kunshe ne cikin wata Sanarwa da Babban sakataren yada labaran Gwamna Malam Abba Anwar ya aikowa Kadaura24.
Sanarwar tace Yayin da Gwamna Ganduje yake kasar Saudiyya mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna zai kasance a matsayin mukaddashin Gwamnan kano.
An umurci dukkan Ma’aikatu, Ma’aikatu da Hukumomi Gwamnatin kano da su yi biyayya da Mukaddashin Gwamna domin tafiyar da jihar yadda ya dace m.
Don haka Gwamna Ganduje ya bukaci kowa da kowa ya yi amfani da kwanaki Goma na karshe na watan Ramalana, domin neman gafarar Allah, da addu’ar samun zaman lafiya ga jihar da kasa baki daya.