Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rashin jin dadinsa akan abinda ya faru a yayin wasan Kano Pillars da Katsina United a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata a Kano, musamman yadda wasu suka farfasa motar Katsina United da kuma tada hargitsi.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Babban sakataren yada labaran Gwamnan Malam Abba Anwar, ya aikowa Kadaura24 a yau dinnan.
Sanarwar Ganduje yace za’a kafa kwamiti mai karfi, kuma za’a samar da sabuwar Mota ga Katsina United, domin mutanen Kano da Katsina duk daya ne, kuma zasu cigaba da kasancewa daya har abada.
Ganduje ya bukaci magoya bayan Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillers zasu daina daukar irin wannnan mumnunan mataki da zai zubar da kimar Jihar kano a idanun duniya.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito magoya bayan Kano Pillers sun fasa motar yan wasan Katsina United bayan Wani wasa da Suka gudanar a filin wasa na sani abacha dake nan Kano.