Ku amfani kuruciyarku kafin tsufa , Mal Umar Sani Fagge ya fadawa Matasa

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Shehun Malamin nan Malam Umar Sani Fagge ya hori Matasa da zu zamu Masu Amfani da lokacin kuruciyarsu wajen yin aiyukan alkhairi Waɗanda al’umma zasu amfana.

Malam Umar Sani ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen taron Kaddamar da Wani littafi Mai Suna Ilajil Wuldan Wanda wani matashi Ammar Nura Mai mukami ya wallafa.

Malamin yace lokaci Yana da matukar muhimmanci a rayuwar al’umma musamman matasa Saboda a Lokacin kuruciyarsu ya kamata su yi abun da zasu yi alfahari da shi bayan girma ya kamasu.

Yace mafi yawa daga cikin malaman Musulunci sun baiwa addinin Musulci Gudunmawa ne lokacin da suke da karancin shekaru,domin a lokacin ne basu da nauyi da yawa akan su.

Malam Umar Sani Fagge ya Kuma tunasar da al’umma muhimmancin yin sallah Wanda dama akan haka aka rubuta littafin, inda yace salla itace aikin na farko da za a tambayi bawa idan ya rasu.

Wanda ya rubuta littafin nan matashi ne don haka ne rokon Matasa a duk Inda suke da su yi koyi da Wannan matashi daya rubuta littafin na ILAJIL WULDAN”.inji Sheikh Umar fagge

Littafin na ilajil wuldan dai yayi bayani ne akan sallah tare da hukunce hukuncanta a addinin Musulci.

Taron ya sama halatar malamai da dama daya cikinsu akwai Shugaban Majalisar malamai ta Jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil da Sheikh Matabuli Nasiru kabara da dai Sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...