Dan Jarida Muhammad Bashir ya Zama Sakatare Janar na tallan takarar Shugaban kasa ta Kingsley Moghalu

Date:

Rukayya Abdullahi Maida
Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya CBN kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar  YPP a zaben 2019, Farfesa Kingsley Moghalu, a ranar Lahadi ya taya sabbin shugabannin kungiyar matasan Moghalu na kasa, Chidinma Mbagwu da Muhammad Bashir murna.
 Kadaura24 ta rawaito Moghalu Youths Coalition, wata uwa ce ta dukkan kungiyoyin an giza manufofin Moghalu a Najeriya, daga yanzu Chidinma Mbagwu ita ce zata jagoranci kodinetan a kasa, Muhammad Bashir kuma zai kasance a matsayin Sakatare Janar na Kungiyar.
 Da yake taya sabbin shugabanin murna a shafin sa na Twitter, Farfesa Moghalu ya ce “Ina taya @OfficialNneoma murna bisa nadin da aka yi mata a matsayin Shugaba @MoghaluYouthCo da Muhammad Bashir @BashirBinBashir a matsayin Sakatare Janar na Kungiyar mu. Ina alfahari da wadannan matasa biyu da tawagarsu, aikin da suka yi a baya shi muke fatan zasu sake yi don nasararmu a 2023.”
https://t.co/jG5NFtG5yg
 Moghalu wanda shi ne jakadi na musamman na shirin ci gaban Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) kan kudi na ci gaban kasashen Afirka bayan yaki da cutar, amma ya yaba da yadda aka yi gaskiya da adalci wajen nada shugabannin biyu. Ya kuma bukace su da su yi aiki tukuru domin ganin ya samu nasara a zaben shugaban kasa na 2023.
 Ana sa ran cewa, wadanda aka nada za su rika kula da ayyukan kungiyar tare da kafa tsarin shugabanci na shiyya da na kananan hukumomi tare da kara wayar da kan jama’a game da manufofin Farfesa Kingsley Moghalu a fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...