Muna daf da sake sakin wasu kudin domin biyan hakkokin yan fansho a kano – Ganduje

Date:

Gwamnatin jihar kano ta yi alkawarin cigaba da biyan kudaden kammala aiki na garatutu ga ma’aikatan da sukai ritaya a jihar nan domin inganta rayuwar yan fansho dake kano.

Kadaura24 ta rawaito Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin taron Manema labarai da ya Gudanar a kano.

Gwamnan Wanda Kwamishinan Kananan Hukumomi na jiha Alhaji Murtala Sule Garo ya Wakilta yace Gwamnatin kano tana sane da halin da yan fansho suke ciki, Kuma tana yin iya bakin kokarin ta don kammala biyan hakkokin Yan fanshon.

Yace bayan kammala biyan rukuni na Farko da Gwamna ya warewa Naira miliyan dubu daya, yace a Wannan Watan ma Gwamnatin zata sake Fitar da wasu kudin domin biya wani rukunin.

“Mai girma Gwamna yana sane Kuma yana kokarin warware matsalolin fansho, Ina baku tabbacin nan bada jimawa ba Gwamnati zata sake sakin Wasu kudin domin a cigaba da biyan yan fansho hakkokin su.” Ganduje

A kokarin Mai da Martani Kan Wani shiri da wasu yan fansho ke yi na Shirya alqunut Gwamna Ganduje yace Gwamnatin Jihar kano baza ta lamunci duk wani Abu da zai kawo tasgaro a sha’anin Zaman Lafiyar da ake da shi a Kano ba.

Gwamnati ba zata nade hannu ba haka Suma Jami’an tsaro ba zasu nade hannu ba wasu bata gari su zo su tayar mana da tarzoma ba, don haka muna gargadinsu da su shiga taitayinsu .” Ganduje

A Jawabinsa Shugaban Hukumar fansho ta Jihar Kano Alhaji Sani Dawaki Gabasawa yace Gwamnatin kano tana kokarin biyan kudin wata-wata na yan fansho,Sannan yace zuwa Ranar talata mai zuwa zasu kammala biyan rukuni na farko hakkokin su.

Yanzu haka mun biya sama da kaso 80 cikin 100 na Waɗanda ya kamata, mun yi tsari sosai ta yadda muke Fara biyan Waɗanda suka Fara shigowa gidan nan kamar yadda mai girma Gwamna yayi umarni”. Inji Dawaki Gabasawa

Shi ma a nasa jawabin Shugaban Kungiyar yan fansho ta jihar kano Salisu Ahmad Gwale yace Kungiyar bata da hannu a shirya aqunutin da ake kokarin yiwa Gwamnati ba, Inda yace su a Kungiyance sun san irin kokarin da Gwamnati ke yi na warware Matsalolin yan fanshon.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...