Ma’aikatar harkokin tsaron Birtaniya ta ce sojojin Rasha sun tabbatar da cewa sun yi amfani da wasu makaman roka da ake kira Vacumm bom wadanda ke zuke iska a Ukraine.
Makaman kan kama da wuta bayan sun zuke iskar wajen da suka fado abin da ke sa su zamo masu matukar hadari.
Ba a haramta amfani da su ba, to amma akwai sharudda kan yadda ake amfani da su.
A baya, Rasha da Amurka sun yi amfani da irinsu a Afghanistan da kuma Vietnam.
Ma’aikatar harkokin tsaron da ke London, ta ce ta yi amanna Rasha ta tura sojojin haya zuwa Ukraine wadanda a baya aka zarge su da aikata cin zarafin bil adama a Syria da Libya da Kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.