Yadda akai Hukumar DSS ta Gayyaci Wasu Jami’an Gwamnatin Kano

Date:

Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci wasu manyan na hannun-daman gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje.

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa mutanen sun kai kansu gaban DSS bisa zarginsu da hannu a dabar siyasa.

Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar ta Kano, Murtala Sule Garo, wanda ya tabbatar wa BBC wannan labarin, ya ce yana cikin manyan jami’an gwamnatin jihar da suka mika kansu ga DSS.

Sauran mutanen sun hada da Fa’izu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Birnin Kano; Khalid Ishaq Diso, shugaban karamar hukumar Gwale; da Injiniya Bashir Kutama, shugaban karamar hukumar Gwarzo.

Murtala Garo ya ce an gayyaci mutumin da ke son jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar ta Kano a zaben 2023, A.A Zaura; da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa; da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi, da kuma wani mai bai wa Gwamna shawara.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wasu daga cikinsu da hannu a manyan-manyan hare-haren dabba, lamuran da suka yi sanadin mutuwar wasu mutane.

Sai dai bayanai sun ce an sallame su.

Ko da a makon jiya, rahotanni sun tabbatar da cewa magoya bayan Murtala Sule Garo da na dan majalisar wakilai Kabiru Alasan Rurum sun yi arangama a karamar hukumar Rano lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama

A baya bayan nan dai ‘yan siyasa musamman na jam’iyyar APC sun rika sukar juna bayan raba gari tsakanin bangaren Gwamna Ganduje da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, sai dai tun kafin hakan an rika jifan juna da muggan kalamai da kuma amfani da ‘yan daba domin biyan bukatu na siyasa.

Hakan kuwa ya yi kamari ne bayan da mai dakin gwamnan jihar Kano, Hafsatu Ganduje, ta yi nuni da cewa Kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo ne ya dace ya gaji mjinta a zaben gwamna na 2023.

‘Yan siyasa da dama sun fassara kalaman da cewa alama ce ta cewa tuni aka ware ‘yan bora da ‘yan mowa kuma an rufe kofa ga duk wanda yake neman zama gwamnan jihar ta Kano a karkashin jam’iyyar APC. To amma daga bisani gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba a fahimci kalaman mai dakin gwamnan ba ne.

Tun daga wancan lokaci ne yanayin siyasa ya kara yin zafi tsakanin bangaren Murtala Sule Garo da kuma Sanata Barau Jibrin, wanda shi ma ake rade-radin yana son tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023.

Kazalika hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke inda ta bai wa bangaren Ganduje nasara a shugabancin jam’iyyar APC a Kano ya ta’azzara yanayin siyasar da ake ciki a jihar.

Masana harkokin siyasa irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge sun ce kokawar neman iko na cikin abubuwan da suka ta’azzara amfani da ‘yan daba wajen cimma buri na siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...